Sri Lanka: An cire dokar sanya kwat da lakataye

Shugaban kasar Sri Lanka Maithripala Sirisena a wani taro
Bayanan hoto,

Shugaban Maithripala Sirisena da sauran 'yan siyasa kan sanya tufafinsu na al'ada, yayin da jami'an gwamnati ke sanya kayan Turawa

Shugaban Sri Lanka ya cire wa manyan jami'an kasar dokar sanya kayan Turawa na kwat da lakataye a wurin taruka da sauran ayyukan gwamnati.

A yayin da yake gabatar da jawabi ga manyan jami'an gwamnati a Colombo ranar Litinin, Shugaba Maithripala Sirisena, ya ce zai janye takardar dokar da tsohon shugaban kasar ya bayar wadda ta tilasta wa manyan jami'an gwamnati sanya kwat da lakataye.

A shekarar 1989 ne tsohon shugaban kasar R Premadasa ya fitar da wata doka inda ya umarci duk wani babban jami'in gwamnati da ya rinka sanya kayan Turawa a yayin harkokin gwamnati.

Da yake sukan tsarin sanya kayan na Turawa Shugaba Sirisena ya bayar da misalin India, inda ya ce, sakatarorin ma'aikatu da manyan Kwamishinoni ba sa sanya kwat ko lakataye, sai dai in ya zama dole.

Shugaban ya ce kamata ya yi doka ko tsarin sanya kayan jami'an gwamnatin kowace kasa ya zo daidai da yanayin zafi ko sanyi da sauran abubuwan da suka danganci kasar.

Yayin da yawancin 'yan siyasa na Sri Lanka ke sanya tufafi na al'adar kasar a tarukan hukuma, jami'an gwamnati suna sanya kayan Turawa ne (kwat da lakataye).

Sai dai su kansu 'yan siyasar idan za su je kasashen waje sukan sanya kayan Turawan ne.

Sri Lanka ta samu 'yancin kai daga Birtaniya a watan Fabrairu na 1948.