Gambia: Minista ya yi murabus domin kyamar Jammeh

Yahya Jameh
Bayanan hoto,

Sai bayan ya amince da shankaye a zaben, sannan shugaba Jameh ya tubure bai aminta da sakamakon zaben ba

Ministan sadarwa na kasar Gambia, Sheriff Bojang, ya sanar da yin murabus daga kujerarsa, a wani mataki na matsa wa Yahya Jammeh lamba da ya sauka daga shugabancin kasar.

Mista Bojang ya ce ya yi hakan ne domin nuna kin amincewa da yunkurin shugaba Yahya Jammeh, na karya dimokradiyyar Gambia.

Sheriff Bojang wanda ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reauters hakan, ya kuma ya yi kira ga sauran masu rike da mukamai irin nasa da su ma su kwata irin abin da ya yi.

Gidan talbijin mallakar kasar dai ya bayyana cewa shugaba Jammeh ya yi wa mista Bojang Korar kare daga aiki ba murabus ya yi ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barrow na da farin-jini sosai a wajen matasa

A yau ne dai ake sa ran kotin kolin kasar za ta fara sauraron karar da shugaba Yahya Jammeh ya shigar yana kalubalantar sakamakon zaben da ya ba wa abokin adawarsa, Adama Barrow nasara, a kansa.

Amma kuma rahotanni na cewa har yanzu alkalan kotun wadanda ake zargin an yi hayarsu daga Najeria da Sierra Leone, ba su kai ga isa Gambiyar ba.

A ranar Litinin ne dai shugabannin wasu kasashe a Afirka ta Yamma suka yi wani taro a Abuja, babban birnin Najeriya, kan makomar siyasar Gambia.

Sun kuma yanke shawarar sake komawa kasar domin lallashin shugaba Jammeh ya mika mulki ranar 19 ga watan Janairun nan.

Shugaban Gambia mai ci, Yahya Jammeh dai ya sauya aniyarsa ta kin amincewa da shan kaye, kasa da mako daya bayan ya amince da faduwa.

Jammeh ya nemi da a sake zabe, a inda kuma sojoji suka karbe ragamar iko da hukumar zaben kasar, bayan da shugaban ya zarge ta da tafka masa magudi.

Wasu dai na danganta kin amincewa da shan kayen da Jammeh ya yi da kalaman da zabbabben shugaba, Adama Barrow ya rinkayi cewa za su bi doka wajen gurfanar da Yahya Jammeh.

Kusan za a iya cewa yanzu haka kallo ya koma kasar Gambia domin sanin abin da zai je ya zo daga ranar 19 ga Janairu, ranar da ya kamata Jammeh ya mika mulki ga Adama Barrow.