Ivory Coast: Ouattara ya kori jami'an tsaro kan bore

Laurent Gbagbo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana yi wa Laurent Gbagbo shari'a bisa zargin aikata laifukan cin zarafin bil adama.

Shugaba Alasanne Ouattara na Ivory Coast ya kori shugabannin sojoji da 'yan sanda da kuma na jami'an tsaron Jandarma.

Hakan dai ya biyo bayan wani bore na kwana biyu da sojoji suka yi wanda kuma ya kassara kasar.

A ranar Juma'a ne dai sojoji suka hau titunan birnin Bouake suna yin bore, kafin daga bisani 'yan uwansu na bariki su mara musu baya, a sauran biranen kasar.

Amincewa da shugaba Alasanne Ouattara ya yi ta biya musu bukatunsu ce dai ta kawo karshen boren.

Boren dai ya faru ne sakamakon gaza biyan sojojin wasu 'yan alawus-alawus dinsu.