Dole mata musulmai su koyi iyo da maza--Kotun tarayyar turai

Switzerland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kotun ta bai wa Switzerland gaskiya a matakinta na bada zartar da tsarin karatun makaranta

Kasar Switzerland ta yi nasara a wata shari'ar kotun kare hakkin bil adama ta tarayyar turai kan wani kudirin da zai tilasta wa iyaye musulmai tura 'ya'yansu mata koyon iyo a azuzuwan koyon linkayan da ke hada maza da mata.

Kotun ta ce hukumomi suna da gaskiya wajen bai wa tsarin karatu da kuma nasarar hadewar yara fifiko.

Kotun ta yarda cewar ta yi katsalandan kan 'yancin addini. Amma alkalanta sun ce ba take 'yancin 'yan adam bane.

Wasu 'yan Switzerland 'yan asalin Turkiyya biyu wadanda suka ki tura yaransu mata ajin koyan linkayar dake birnin Basel su ne suka shigar da karan.

Sai dai kuma Jami'an ilimi sun ce dokar bata shafi yara mata wadanda suka mallaki hankalin kansu ba, kuma yaran da iyayensu suka shigar da karan basu kai shekarun ba a lokacin.

A shekarar 2010 ne bayan cece-kuce mai tsawo aka umurci iyayen su biya kudin Switzerland 1,400 domin sakaci da aikinsu a matsayinsu na iyaye.