FIFA ta kara yawan kasashe a gasar kofin duniya zuwa 48

FIFA

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino ya ce ya kamata gasar cin kofin duniya ta kara fadada

A bisa sabon tsarin, rukuni 16 mai tawagogi uku ko wanne za a samar a matakin farko kafin a kai matakin kifa-daya-kwala inda tawagogin da suka kai labari 32 za su fafata idan aka fara amfani da sauyin a gasar shekara ta 2026.

Hukumar kwallon kafar ta duniya ta yi ittifaki wajen kada kuri'ar amincewa da kawo sauyin ne yayin wata ganawar da a ka yi a birnin Zurich ranar Talata.

Yawan wasannin da za a buga zai karu zuwa 80 daga 64, amma wadanda suka yi nasara za su yi wasanni bakwai ne kawai kamar yadda ake yi a yanzu.

Za a kammala gasar a cikin kwanaki 32 - a wani mataki na kwantar da hankalin wasu kungiyoyin kwallon kafa na Turai masu karfin fada-a-ji, wadanda ba su goyi bayan a yi garambawul din ba saboda cunkoso a jadawalin wasanni na duniya.

Wannan ne mataki na farko da aka dauka don fadada Gasar cin Kofin Duniya tun shekarar 1998.

Dalilin Karin

Shugaban FIFA Gianni Infantino ne ya kirjin bikin neman kawo sauyin, yana cewa ya kamata Gasar cin Kofin Duniya ta kunshi kowa da kowa.

Da yake jawabi a wurin wani taro a kan wasanni a Dubai a watan Disamba, Infantino ya ce matakin fadada gasar zai kawo ci gaba a harkar kwallon kafa a duniya baki daya.

Ya kara da cewa: "Babu abin da zai bunkasa harkar kwallon kafa a kasashe fiye da shiga Gasar Kofin Duniya".

Duk da fadin sa cewa "bai kamata shawarar ta zama don kudi aka yi ba", Infantino ya yi bayani a kan yiwuwar samun karin kudin.

Wani bincike da hukumar ta gudanar ya yi hasashen kudaden shigar da hukumar ke samu zai karu zuwa sama da fam biliyan biyar ga tawagogi 48 da yiwuwar samun karin riba zuwa fam miliyan 521.