Gambia: Kotun koli ta dage zamanta kan batun zaben shugaban kasa

Gambia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yahyah Jammeh ya mulki kasar Gambia har na tsawon shekaru 22

Kotun kolin Gambia ta dage zaman da ta tsara gudanarwa kan zaben shugaban kasar zuwa watan Mayu, saboda rashin halartar isassun alkalai.

A yau ne aka tsara, kotun za ta saurari karar da shugaba Yahya Jammeh ya shigar bayan ya ki amincewa ya karbi kayen da aka yi masa.

A yayin gudanar da zaben, kotun kolin na da tabbataccen alkali guda daya ne kawai.

An tuntubi alkalai da dama daga kasashe makwabta, sai dai har yanzu ba su kai ga isa kasar ba.

A jiya Litinin, ministan yada labaran kasar, ya sanar da ajiye mukaminsa don nuna adawa da matakin Yahya Jammeh na kin karbar sakamakaon zaben.

Wani taron wasu shugabannin kasashen Afirka ta yamma ya aika ayarin shugabannin a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari na Nijeriya don su je kasar a gobe su bukaci Yahya Jammeh ya sauka daga mulki cikin girma da arziki.