Ghana: Mahama ba shi da damar ci gaba da zama a gidansa

Ghana John Mahama

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A watan da ya gabata ne Mahama ne Mahama ya fadi a zabe

Tsohon shugaban kasar Ghana John Mahama ba shi da damar ci gaba da zama a gidan da yake tun lokacin yana kan mulki, in ji wani mai kusanci da sabon shugaban kasar.

Rashin fita daga gidan da Mr Mahama ya yi bayan karewar wa'adin mulkinsa ranar Asabar ya haddasa gagarumin rudani a kasar ta Ghana.

A wata sanarwa da ya fitar, ofishin Mr Mahama ya ce an cimma yarjejeniya da tawagar Mr Nana Akufo Addo a watan da ya gabata cewa zai ci gaba da zama a gidan.

Mataimakin shugaban kasar Muhamudu Bawumia ne ake sa ran zai koma gidan, da ake yiwa lakabi da Australia House, amma yana zaman jira.

An dai jinjinawa Mr Mahama a fadin kasar, kan amincewa da shan kaye da ya yi a zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin watan da ya gabata, a maimakon kalubalantar sakamakon zaben.

Yana daga cikin masu shiga tsakani da ke kokarin shawo kan tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh da ya amince da shan kayen da ya yi a zaben da ya gabata.