Ana zargin Goodluck Jonathan da karbar biliyoyin daloli

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masu shigar da karar sun ce wadanda suka ci moriyar kudin sun sayi gidaje da jiragen sama da motoci masu silke

Masu shigar da kara a kasar Italiya na zargin tsohon shugaban Nigeria Goodluck Jonathan da tsohuwar ministar albarkatun mai Diezani Alison-Madueke da karbar kudade da yawansu ya kai $1.3 biliyan.

Ana zargin Jonathan da Diezani da karbar kudin ne a wata badakalar rijiyar man da ta shafi kamfanonin mai na ENI da Shell.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce, a wasu bayanai da kotu ta tara a watan da ya gabata a birnin Milan, ta shigar da karar sunayen mutane 11 wadanda suka hada da manyan ma'aikatan kamfanonin man da kuma kamfanonin biyu.

Sunayen Jonathan wanda ya sauka daga kan mulki a shekarar 2015 da Diezani , wace ta shafe tsawon lokacin a matsayin ministarsa ta albarktun mai basa cikin jerin sunayen da aka shigar da kararsu.

Amma ana zargin sun taka muhimmiyar rawa a badakalar wanda kamfanonin mai na ENI da Shell suka karbi $1.3 biliyan na wata rijiyar mai da ke cikin teku a Najeriya a shekarar 2011.

Ba a kama su da laifi ba a hukumance kuma wadanda ake tuhumar suna da dama ta tsawon kwanaki 20 su mayar da martani a kan rahoton binciken kafin a shigar da kara a hukumance.