Uganda: Museveni ya nada dan sa a matsayin mai ba shi shawara

Janar Muhoozi Kainerugaba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An zargi Museveni cewa dansa Muhoozi Kainerugaba na daya daga cikin hanyoyin kafa daular siyasa

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya nada dan sa Janar Muhoozi Kainerugba a matsayin mai ba shi shawara.

Janar Kainerugaba ya kasance jagoran rundunar soji ta musamman da ke lura da harkokin tsaron mahaifinsa, bayan da ya samu karin girma ta hanyar matsayin da yake da shi.

An sha sukar lamirinsa kan bai wa 'yan uwansa manyan mukamai.

Kanensa daya daga cikin masu bai wa shugaban kasa shawara ne, kana matarsa ministar ilmi da harkokin wasanni ce.

Babban hafsan tsaron kasar Gen Katumba Wamala ya rasa mukaminsa, inda aka bashi mukamin karamin minista a gwamnatin.

Ya rike mukamin soji mafi girma a kasar ta Uganda, don haka ana kallon sabon mukamin da aka ba shi a matsayin mayar da shi baya.

Kakakin rundunar sojin kasar ya ce sauye-sauyen abu ne mai kyau ga ci gaban kasa.