Mutane da dama sun nutse a Tanzania

Masu ceton

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutane 12 ne suka rasa rayukansu a lokacinda jirgin ya kife

Mutane 40 sun rasa rayukansu bayan jirgin ruwan da suke tafiya a ciki ya kife a hanyarsu daga garin Tanga dake bakin ruwa zuwa tsibirin Pemba a daren Litinin.

Shugaban 'yan sandan lardin arewa maso gabas, Benedict Wakulyamba, ya shaidawa BBC cewa jirgin na dauke da mutane 50.

Shugaban 'yan sandan ya ce an ceto mutane tara kuma an gano gawarwaki guda 12.

Ba a tabbatar da abin da ya haddasa kifewar jirgin ba, amma Benedict yace mai yiwuwa iska mai karfi ce ta kifar da jirgin ruwan.