Morocco ta haramta sanya burka

Wasu mata sanye da burka a

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Yawancin mata a Moroko sun fi amfani da hijabi, maimakon burka

Moroko ta haramta dinkawa da sayarwa da kuma shigo da da burka kasar kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.

A ranar Litinin aka aika wa 'yan kasuwa da sauran masu dinkawa da sayar da burkan wasikun haramcin, inda aka umarce su da su rabu da duk wanda suke da shi cikin sa'o'i 48.

Ko da yake ba wata sanarwa ta hukuma kan haramcin, amma an ruwaito wasu jami'an gwamnati da ba a bayyana sunansu ba, da suka ce an dau matakin ne domin tabbatar da tsaro.

Ba a dai san ko gwamnatin kasar tana son haramta burkan ba ne kai tsaye.

Wani babban jami'in ma'aikatar harkokin cikin gida ya tabbatar da haramcin ga shafin kafar yada labarai ta intanet na Le360.

Kuma ya kara da cewa mahara suna amfani da tufar ta burka wajen aikata miyagun laifuka.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Hukumomin kasar ta Moroko ba su fito da wata sanarwa ta haramcin ba

Yawanci mata a kasar ba sa amfani da burka, wanda ke rufe jiki gaba daya, a maimakonsa sun fi amfani da hijabi, wanda shi ba ya rufe fuska.

Matakin ya raba kan mutane a kasar ta arewacin Afirka, wadda Sarki Mohammed na shida mai ra'ayin sassauci, ke shugabanta.

Wani mai wa'azin Musulunci Hammad Kabbaj,wanda aka hana tsayawa takarar majalisar dokokin kasar a watan Oktoba, kan zargin dangantakarsa da masu tsattsauran ra'ayin Musulunci ya yi watsi da haramcin.

Ya kuma soki hukumomin Morokon da yin bakin-ganga, ta yadda suka amince da mata su rika sanya matsattun kaya irin na wanka a tafki, ko shakatawa a bakin tekum, a matsayin 'yancin da ba za a hana ba.

Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta arewacin kasar ta Moroko, Northern Moroccan National Observatory for Human Development, ta ce ta dauki dokar a matsayin tauye 'yancin mata na sanya tufar da ta dace da addininsu ko siyasarsu ko al'adarsu.