Biri na barbara da gada a Japan

Biri na saduwa da gada a Japan
Bayanan hoto,

Birin ya sadu da gada akalla biyu

A kasar Japan an dauki hoton wani biri irin jinsin da aka fi samu a kasar, a lokacin da yake kokarin yi wa wata gada barbara, wanda abu ne da ba a saba gani ba.

Masu binciken kimiyya sun ga birin a lokacin da ya ke kokarin saduwa da gada har akalla sau biyu, a watan Nuwamba na 2015, a lokacin barbarar biran.

Biran sukan yi wanka a wata korama ta ruwan zafi a wani yanki na Japan da dusar kankara ke zuba a Japan, kuma suna rayuwa tare da sauran dabbobin dawa irin su gada a wurin.

An ruwaito labarin wannan dabi'ar ta birin wadda ba a saba gani ba a mujallar nazarin birai ta Primates.

Wannan ba shi ne karon farko na yadda wata dabba ke kokarin barbara da wata dabbar da ba jinsinta ba.