Kun san abin da ke sa tsofaffi su ji daɗin barci?

older man yawning

Asalin hoton, Thinkstock

Masana kimiyya sun shawarci mutanen da suka kai shekara 50 zuwa sama da su kauracewa shan gahawa ko kofi bayan cin abincin rana idan dai suna so su yi bacci mai dadi da daddare.

Wani rahoto da kungiyar masana kan lafiyar kwakwalwa ta charity Age da ke Birtaniya ta fitar ya ce samun bacci mai dadi yana yi wa tsofaffi wahala amma samun isasshen hutu zai taimaka wa kwakwalwarsu ta rika tunani mai kyau.

Rahoton ya bai wa tsofaffi shawara su rika yin baccin awa bakwai zuwa takwas da daddare, sannan suka fitar da hanyoyin da suke gani idan an bi su za a tabbatar da hakan.

Baya ga daina shan gahawa, rahoton ya bukaci tsofaffi su takaita kalular da suke yi da rana zuwa kasa da awa daya.

Sauran shawarwarin su ne:

  • Su rika tashi daga bacci a lokaci daya kowacce rana
  • Su rika shan hantsi
  • Kada su sha giya
  • Su ci abincin dare awa uku kafin su yi bacci
  • Kada su rika karatu ta kwamfuta ko wayar salula ko kwamputar tebur kafin su kwanta bacci
  • Su gujewa yin amfani da magungunan da ba likita ne ya ce a yi amfani da su ba
  • Su rika sanya safa a kafafunsu kafin su yi bacci
  • Kada su yi bacci tare da daddobin gida irin su kyanwa
  • Su gujewa yin musu da matarsu ko mazajensu kafin su kwanta

Asalin hoton, Thinkstock