Goodluck Jonathan ya musanta karbar cin hanci

Jonathan da Diezani

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnatin Najeriya tana bincike kan mukarraban gwamnatin Jonathan

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, ya musanta karbar cin hancin a cikin dala biliyan 1.3 wanda ake bincike a kai a Italiya.

Kakakin shugaban kasar Ikechukwu Eze ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar ranar Talata inda ya ce ba a tuhumar Mista Jonathan kan karbar kudin haramun a wata badakalar rijiyar mai a Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewar tsohon shugaban kasar ba shi da kadarori a kasashen waje.

Ikechukwu Eze ya ce, "Za mu so mu sake nanatawa cewar lokacin da yake gwamnati da lokacin da ya bar gwamnati, tsohon shugaba Jonathan ba shi da wani asusu a kasashen waje ko jirgin sama ko kuma wata kadara. Mun kalubalanci duk wani mai bayanin da ke nuna akasin hakan da ya buga shi."

Masu gabatar da kara a Italiya sun fitar da wasu takardun kotu wadanda suka ayyana zaman tuhumar manyan kamfanonin mai da mutum 11 da laifi, inji kamfanin dillacin labaran AFP.

Babu sunayen Mista Jonathan, wanda ya bar karagar mulki a watan Mayun 2015, da kuma ministarsa ta mai, Diezani-Alison-Madueke a jerin sunayen da ake tuhuma da laifin.

Amma masu gabatar da kara sun yi zargin cewar sun taka muhimmiyar rawa a badakalar inda aka ba da dala miliyan 466 ga jami'an gwamnati - ciki har da Mista Jonathan da Mis Alison-Madueke.