Mourinho ya nemi 'yan United su yi himma a wasan su da Liverpool

Jose Maourinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jose Maourinho yana son 'yan wasan sa su zage dantse a wasan da za su yi ranar Lahadi

Kociyan Manchester United, Jose Mourinho, ya sanar da masu sha'awar kungiyarsa cewar wasan kungiyar da abokan gogayya Liverpoo ranar Lahadi ba abin nishadi ba ne kawai.

United ta doke Hull City da 2-0 a kafar farko a wasansu na kusa da na karshe a gasar cin kofin EFL ranar Talata inda Juan Mata da Marouane Fellaini suka sha kwallaye daddaya bayan hutun rabin lokaci.

Duk da haka, Mourinho ya ce dole kowa ya kara kokari a wasan da za a yi da Liverpool.

"Muhimmin wasa ne gare mu," in ji shi.

"Idan muka kara kaimi a wasan, masu sha'awarmu za su zo su yi wasa da mu. Idan ba mu yi wasa da jikinmu ba, masu kallonmu ba za su yi ihu ba.

"Amma muna da masu sha'awarmu masu matukar ban mamaki wadanda suke karfafa mana gwiwa.

"Kowa yana son manyan sunaye - 'yan wasa da manajoji da masu kallo. Kowa yana son manyan wasanni. Saboda haka bari mu tasamma babban wasan ranar Lahadi".

United za su karbi bakuncin Liverpool da karfe 4:00 a agogon GMT suna masu neman tsawaita nasarorinsu zuwa 10 a jere a gasar Premier.

'Yan wasan Jurgen Klopp su ne na biyu a teburin gasar Premier inda suke gaban United da maki biyar.