Philippines: Za a raba wa mata magunguna hana daukar ciki a kyauta

Gwamnati ta ce tana yunkurin tabbatar da shirin kayyade iyali

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Gwamnati ta ce tana yunkurin tabbatar da shirin kayyade iyali

Shugaban Philippines ya umarci ma'aikatun kasar su rika bai wa matan da ba su da hali da suka kai miliyan shida magungunan hana daukar ciki a kyauta.

Shugaba Rodrigo Duterte ya ce ya dauki matakin ne domin ya rage yawan matan da ke daukar ciki ba tare da niyya ba, musamman talakawa.

Sai dai ana sa ran wannan mataki zai fuskanci kalubale daga wajen Cocin Roman Katolika.

Mutumin da Duterte yagada ya kwashe shekaru da dama wajen ganin an amince da kudirin dokar da zai bayar da dama a rika amfani da magungunan hana daukar ciki.

Sai dai kotun kolin kasar ta dakatar da raba magungunan hana daukar cikin na dan wani lokaci a wata doka da ta yi a shekarar 2015 bayan kungiyoyin hana amfani da magungunan daukar ciki sun nuna kin amincewar su.

Amma gwamnati ta daukaka kara a kan batun.

Sama da kashi 80 cikin 100 na 'yan kasar ta Philippines mabiya Cocin Roman Katlika ne, a cewar wani bincike da cibiyar Pew ta gudanar.