Ko kun san 'yan sandan China ba sa murmushi?

Ana zargin 'yan sandan Xi'an da nuna rashin da'a

Asalin hoton, China Photos/Getty Images

Bayanan hoto,

Ana zargin 'yan sandan Xi'an da nuna rashin da'a

Hukumomi a birnin Xi'an na kasar China sun soma bai wa 'yan sandan birnin horo kan yadda za su rika nunawa mutane karamci a lokacin aiki.

Horon, wanda ake yin sa a wani babban otal, zai nunawa 'yan sanda hanyoyin da za su rika yin murmushi ga jama'a.

Rundunar 'yan sandan gundumar Chang'an ce ta dauki matakin bayan wani gidan talabijin ya nuna wasu 'yan sanda suna nuna rashin girmamawa ga wasu mutane, a cewar jaridar Sanqin Daily.

Shafin sada zumunta na Weibo ya ambato rundunar 'yan sandan na cewa an tura 'yan sanda 20 zuwa otal din domin su samu horo na wata uku kan yadda za su sauya salon aikinsu.

Shafin ya wallafa wasu hotuna na abubuwan da ke faruwa a otal din, wadanda suka nuna 'yan sandan a kusa da masu karbar baki.