Kremlin: Rasha ba ta da bayanan sirri game da Trump

Donald Trump

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Donald Trump ya caccaki rahotannin da ke cewa Rasha ta saci bayanan Amurkawa

Fadar gwamnatin Rasha ta musanta zargin cewa hukumomin leken asirin kasar sun samu wasu bayanai da ba za a so gani ba game da shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump.

Ƙakakin shugaba Vladimir Putin, Dmitry Peskov, ya ce zargin "mai ban dariya ne wanda ke kokarin ya lalata dangantakarmu".

Rahotani dai sun nuna cewa Rasha tana da bayanai a kan Mr Trump da suka shafi karuwai da wasiku a kan sirrin neman shugabancinsa.

Mr Trump ya soki rahotannin da cewa ba su da inganci.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Shugaba Putin da Trump sun yi hira kan dangantakarsu

Shugaban Amurka mai jiran gadon ya bayyana a shafin shi na Twitter cewa: "Wannan labari karya ne."

Ana sa ran Mista Trump zai yi jawabi ga wani taron manema labarai ranar Laraba, kwana tara kafin ya dare karagar mulki.

Manufar taron ita ce ya mayar da hankali ga yunkurin Mista Trump na yanke duk wata alaka tsakaninsa da harkokin kasuwancinsa, da kuma mayar da martani ga damuwar da ake nunawa game da yiwuwar a matsayinsa na shugaban kasa ya yanke hukuncin da zai amfani harkokinsa na kashin kansa.

Satin da ta wuce hukumomin leken asirin Amurka sun gabatar da rahoto da ke muna cewa Rasha ta yi kutse a imel din kwamitin yakin neman zaben Hillary Clinton da zummar kunyata ta, zargin da ta sha musantawa.