Gambia: Shugaba Jammeh ya sha alwashin ci gaba da mulki

Yahya Jammeh

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Jammeh ya yi kira ga 'yan Gambia su yi hakuri har kotu ta yanke hukunci

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya sha alwashin cewa 'zai zauna a kan kujerar mulki har sai an yanke hukunci a kan sakamakon zaben shugaban kasar'.

Shugaba Jammeh ya ce ba zai sauka daga kujerar mulki ba sai bayan Kotun Koli ta yanke shawara a kan jayayyar da yake yi da sakamakon zaben, karar da sai a watan Mayu za a saurare ta.

A wani jawabi da ya yi ta gidan talibijin na kasar, ya jaddada rashin amincewa da katsalandan din da kasashen waji ke yi a harkar cikin gida ta kasar.

Wata tawagar ECOWAS a karkashin jagorancin shugaban kasar Nijeriya za ta kai ziyara Gambia ranar Juma'a don kara matsawa Yahya Jammeh lamba don ya mika mulki ga Adama Barrow bayan zaben watan Disamban bara.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Shugabannin kasashen Afrika ta yamma sun gana da Yahya Jammeh a watan Disamba za kuma su sake komawa ranar Juma'a.

Shugaba mai jiran gado Adama Barrow ya ce za a kaddamar da shi a mako mai zuwa.

Mista Jammeh, wanda ya kwashe shekaru yana mulki, da farko dai ya amince ya mika mulki bayan an kayar da shi a zaben, sai dai kuma daga bisani ya ce bai amince da sakamakon ba saboda wasu kurakurai da aka ce an gano wajen hada alkaluman.

Amma hukumar zaben ta jaddada cewa kuskuren bai shafi sakamakon ba kuma Mista Barrow ne ya lashe zaben.

Tun 1994 Mista Jameh ke mulkin kasar Gambia, kuma ana zargin shi da tauye 'yancin bil'Adama duk da cewa yana gudanar da zabe a-kai-a-kai.