An samu matukar raguwar'yan gudun hijira a Jamus

'Yan gudun hijira

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An sa siyasa sosai a cikin batun 'yan gudun hijira a Jamus

Jamus ta ce 'yan gudun hijira 280,000 ne suka shiga kasar a cikin shekarar 2016, amma sama da 'yan gudun hijira 600,000 sun ragu idan aka kwatanta da shekarar 2015.

Ministan harkokin cika gida na Jamus ya ce 'yan gudun hijirar sun ragu ne sakamakon rufe hanyar Balkan da aka yi da kuma yarjejeniyar 'yan gudun hijira tsakanin Turai da Turkiya.

An samu mutane 890,000 da ba a taba samun yawansu ba sakamakon 'yan gudun hijira da 'yan ci rani da suka shiga Jamus ta kasar Greece da Balkans.

Sun nufi Jamus bayan shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci a samar da wata manufa da za ta bai wa masu neman mafaka dama na wucin gadi.

Ta yanke Shawarar dakatar da matakan da Turai ta dauka na yin rijistan masu neman mafaka a jihar Turai ta farko da suka shiga ne saboda yawan 'yan Syria da suke tserewa daga kasarsu saboda rikici, amma akasarin mutane 'yan wasu kasashen sun yi nasarar tafiyarsu.