Kungiyoyin agaji na almubazzaranci —Shettima

'Yan gudun hijira

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dubun dubatar mutane na zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a arewa maso-gabashin Najeriya

Akasarin hukumomin agaji da ke Arewa maso gabashin Nigeria na facaka da kudin da ya kamata a yi amfani da su wajen kulawa da wadanda rikicin Boko Haram ya ritsa da su a cewar gwamna Kashim Shettima na jihar Borno.

Kashim ya kara da cewa kungiyoyi 126 wadanda aka yi wa rijista a jihar ne ke aiki kamar yadda ya kamata, domin taimaka jama'a.

Ya soki hukumar da ke kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya da sayen motoci masu sulke , inda ya kara da cewa shi baya amfani da irin wadan nan motocin.

A watan da ya gabata ne majalisar ta nemi da a taimaka mata da dala biliyan daya domin ta agazawa masu fama da matsananciyar yunwa a yankin.

Majalisar dinkin duniya ta ce akwai yi wu war kusan sama da mutane miliyan biyar da ke jihohi uku a Arewa maso gabashin kasar za su fuskanci karancin abinci saboda manoma ba su yi shuka ba shekara uku a jere.

Manoman suna tsoron watakil kungiyar Boko Haram ta saka abubuwan da za su iya fashewa a gonakin nasu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa kananan yara za su iya rasa rayukansu, sai dai idan sun samu agajin gaggawa

Ana bukatar agajin gaggawa ga mutane 100,000 wadanda akasarinsu suke fuskantar hadarin mutuwa saboda matsanancin yunwa.

A shekarar 2014 ne sojojin Najeriya suka kwato akasarin yankunan da ke karkashin ikon 'yan Boko Haram, amma dubban mutanen da suka bar gidajensu na zama a sansanonin 'yan gudun hijira.

Sai dai gwamna Shettima ya ware wasu kungiyoyi da ke kokari kamar ta samar da abinci ta majalisar dinkin duniya da kwamitin Red Cross na duniya da wadda ke kula da hijira ta duniya da mai kula da masu neman mafaka ta kasar Norway da Denmark.

Shettima ya ce "Kungiyoyi da ke neman ci da gumun al'ummar mu suyi gaba".

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ce gwamnan ya yi wannan furucin ne ga 'yan majalisa da manema labarai a daren Talata a majalisar dokokin Jihar Borno dake birnin maiduguri.