ECOWAS na lalubo hanyoyin dakile safarar kudaden haram

Kwamitocin kudi na majalisun dokokin kasashen ECOWAS ne ke taron

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

ECOWAS na fatan ganin kasashe sun hada hannu wajen yaki da safarar kudaden haram

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, na neman hanyoyin da za ta bi domin magance matsalar safarar kudaden haram a tsakanin kasashen yankin.

Kwamitocin kudi na majalisun dokokin kasashen kungiyar ne ke nazarin hanyoyin, a wani taron kwana uku da suke yi a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, wanda a ranar Alhamis din nan suke kammala shi.

Taron na tattaunawa ne a kan matsalar zirga zirgar kudaden da ake samu ba a kan ka'ida ba,matsalar da bincike ya tabbatar ta yi kamari a Afirka.

A karshe taron na sa ran fadakar da kasashe a kan muhimmancin da ke akwai na samar da dokokin hukunta masu hannu a safarar irin wadannan kudade.