Mali: Jamus za ta tura karin sojoji

Wasu daga cikin dakarun zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Mali

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Yanzu yawan sojojin Jamus a cikin dakarun Majaliasr Dinkin Duniya a Mali zai kai 1000

Majalisar dokokin Jamus ta amince da shirin tura karin sojojin kasar zuwa Mali domin shiga rundunar tabbatar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, (MINUSMA).

Wannan zai sa yawan sojojin Jamus ya kai 1000 daga cikin jumullar sojin tabbatar da zaman lafiyar na Majalisar Dinkin Duniya 15,000.

Idan majalisar Jamus din ta amince da tura karin sojojin, to wannan zai zama lokaci na farko da kasar ta tura sojoji mafi yawa wani aiki a waje.

To amma kusan sojoji 100 ne na rundunar tabbatar da zaman lafiyar suka mutu a Mali, yawanci a hare-haren da masu ikirarin Jihadi da ke da alaka da kungiyar Alka'ida ke kai musu.

Bayanan hoto,

Mayaka masu ikirarin Jihadi sun hallaka sojin Majalisar Dinkin Duniya kusan 100 a Mali

Babban aikin rundunar Majalisar Dinkin Duniyar a Mali, shi ne, sanya ido wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Mali da 'yan tawaye.

To amma kasancewar dimbin mayakan 'yan gwagwarmaya masu ikirarin Jihadi a yankin arewacin kasar, na nufin wannan ba aiki ne mai sauki ba.

Wannan ne ma ya sa aikin ya kasance mafi hadari ga dakarun Majalisar Dinkin Duniya a yanzu.

Wannan ne ma ya sa Jamus din yanke shawarar tura karin sojoji kasar ta Mali, inda za su yi sansani a garin Gao, da ke arewa maso gabashin Malin.

Jamusawan za su rika aiwatar da aikin leken asiri da sanya ido, ta kasa da kuma ta sama, ta amfani da jirage marassa matuka.

Kasar za ta kuma aika da jirage masu saukar ungulu domin fafata yaki da kuma aikin ceto, inda za su maye gurbin, takwarorinsu na kasar Holland ko Netherlands.

Yanayin hamada na arewacin Mali ya sa ake bukatar samar da jiragen sama na musamman da kwararrun masu sarrafa su, domin taimaka wa dakarun kasa.

A watan Oktoba da ya wuce shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel ta yi alkawarin ba wa Mali taimako wajen yaki da masu ikirarin Jihadi.

A lokacin ne kuma shugabar ta bayyana shirin kasar ta Jamus na kafa wani sansanin soji a makwabciyar Malin, Nijar.