Tsuntsaye za su hana jirage tashi a Lebanon

Filin jirgin sama na Beirut

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dandazon tsuntsayen da ke taruwa a filin jirgin saman sakamakon sharar da aka tara kusa da shi na saka jiragen da ke sauka a filin jirgin saman Beirut cikin hadari.

Akwai yiwuwar jiragen sama a filin jirgin Beirut, babban birnin kasar Lebanon na cikin hadari bayan tsuntsaye sun fara tashi a wurin wata shara mai yawa da aka tara kusa da filin jirgin saman.

Ministan sufurin kasar, Yusef Fenianos ya ce an tursasa wa kasar fuskantar dokar ta-baci yayin da tsuntsaye ke ci gaba da da sauka a yankin.

Wata kafar yadda labarai na kasar ta ce a ranar Talata wani jirgin sama na gabas ta tsakiya ya samu matsala a lokacin da ya sauka a bangaren yamma na filin jirgi saboda dandazon tsuntsaye.

Masu fafutika sunyi kira da a rufe wajen zubar da sharan kafin a samu afkuwar hatsarin jirgi.

An samar da wurin zubar da sharan, wanda ake kira Costa Brava ne a watan Maris din shekarar 2016, domin shawon kan matsalar sharar da birnin ke fama da ita.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An samar da wurin tara shara na Costa Bravo ne domin magance matsalar sharar da ke taruwa a kan titunan Beirut

Tarin shara dake kan titunan na kai wa yawan tan 20 a lokutan da aka fi zafi a cikin shekara.

Rahotanni sunce jinkirin da kasar ke yi wajen samar da ma'aikatar sarrafa shara a Costa Brave, inda ake tara sharar ne ke haddasa tarin dake kaiwa yawan mita 9.

Masu fafutukar kare muhalli sun kwashe watanni suna gargadin cewar sharar na jawo beraye da dandazon tsuntsaye , yayin da a watan Agusta, kungiyar matuka jiragen sama na kasar Lebanon suka yi zargin yiwuwar injinan jirgi za su iya zuke su.