An dakatar da wasu likitoci a Kenya

Likita a Kenya
Bayanan hoto,

A ranar Alhamis ne likitoci ke tattaunawa domin shawo kan matsalar

An dakatar da wasu likitoci 6 tsawon wata daya saboda kin janye yajin aiki da kungiyarsu ke yi.

Jaridar Daily Nation ta rawaito cewar yajin aikin yasa aikace-aikacen asibitocin gwamanti na kasar na fuskantar nakasu.

Kotun dake sansantawa kan harkar kwadago ta bai wa kungiyar umarnin ta kawo karshen yajin aikin kuma ta kammala yarjejeniya tsakaninta da gwamnati a cikin makonnin biyu.

An sha yin yunkurin kawo karshen yajin aikin amma abin ya ci tura, saboda likitocin suna so a aiwatar da wata yarjejeniya da aka sakawa hannu a shekarar 2013 wadda za ta inganta aikin likitoci kuma ta sa a kara musu albashi.

Alkalin kotun Hellen Wasilwa ta ce idan har jami'an ba su bi umarnin da ta gindaya musu ba, za a kulle su a gidan yari na tsawon makonni biyu.