'Yan wasa uku sun sabunta kwantaraginsu a Arsenal

Giroud

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Giroud na taka rawa a Arsenal

'Yan wasan Arsenal guda uku Olivier Giroud, Laurent Koscielny da kuma Francis Coquelin sun sanya hannu a kan yarjejeniyar tsawaita zaman su a kungiyar.

Arsenal ba ta fadi yawan shekarun da Giroud, mai shekara 30, da Koscielny, mai shekara 31, da kuma Coquelin, mai shekara 25 za su kara kwashewa a kungiyar ba.

Sai dai a wani sakon Twitter da Koscielny ya wallafa ya ce zai tsawaita zaman sa a kungiyar zuwa shekarar 2020.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce, "Muna matukar murnar cewa 'yan wasan uku masu muhimmanci ga kungiyarmu sun amince su ci gaba da zama a nan har lokaci mai tsawo."

'Yan wasan uku 'yan kasar Faransa na cikin wadanda aka fi sanya wa a wasa.