Nana Akufo-Addo ya nada ministoci

Nana Akufo-Addo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An rantsar da Mr Akufo-Addo ranar Asabar bakwai ga watan Janairu na shekarar 2017.

Sabon shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya fitar da rukuni na biyu na ministoci wadanda ke jiran tantancewa daga majalisar dokoki.

Shugaba Nana ya fitar da sunayen ministoci 25, wadanda a cikinsu shida sabbi ne da ya kirkiro.

Sai dai wani dan majalisar dokokin kasar mai wakiltar Bawku ta tsakiya, Dr Hassan Ayariga bai amince da nadin ministan ministoci ba.

Ya kara da cewa babu inda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar da ministan ministoci.

Malam Muhammad Abbas na makarantar kimiyya da siyasa dake garin Kumasi ya ce akwai yiwuwar shugaban ya nada ministan ministoci ne saboda kwarewarsa da kuma zurfin iliminsa.

Ya kuma kara da cewa a ka'idar kundin tsarin mulkin kasar, Nana Addo yana da ikon ya nada ministocin da yake so kuma ya kirkiri ma'aikatun da yake so.

Shugaba Addo ya sha alwashin kirkiro karin sabbin yankuna guda hudu nan da farkon shekarar 2018.

A farkon watan jiya ne dai hukumar zaben Ghana ta bayyana jagoran 'yan adawan a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi.

Labarai masu alaka