An bai wa mataimakin Obama, Joe Biden, babbar lambar yabo

Joe Biden da Barack Obama Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Obama ya yi raha inda ya ce wannan ne lokaci na karshe da zai rungumi Biden

Shugaban Amurka Barack Obama ya bai wa mataimakinsa Joe Biden, wanda ke cike da mamaki, lambar yabo ta Medal of Freedom, mafi girma da ake bai wa duk wani farar-hula a kasar.

Mr Obama ya yaba wa Mr Biden matuka saboda abin da ya kira "imanin da ka yi da sauran Amurkawa da kuma kauna da ka nuna wa kasarka a lokacin da kake aiki".

An bai wa Mr Biden lambar yabon ne a yayin da dukkaninsu su biyun ke shirin sauka daga mulki ranar 20 ga wannan watan.

Mr Biden ya ce zai ci gaba da kasancewa cikakken dan siyasa a jam'iyyar Democratic Party.

'Ya sha mamaki'

Joe Biden, wanda a fili ya nuna matukar sosa ransa a lokacin da Mr Obama ya ba shi lambar yabon, ya ce shugaban kasar shi ne "mutumin da ya fi dacewa Amurkawa su zaba domin ci gaban kasarmu" a lokacin da aka zabe shi.

Jaridar New York Times ta ce lambar yabon da aka bai wa Joe Biden tana da matukar muhimmanci.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Obama ya yi raha inda ya ce wannan ne lokaci na karshe da zai rungumi Biden

Labarai masu alaka