Ana take hakkin bil-adama a Najeriya -Human Rights Watch

Gwamnatin Najeriya ta sha musanta zargin da kungiyoyin kare hakkin dan-adam ke mata
Bayanan hoto,

Gwamnatin Najeriya ta sha musanta zargin da kungiyoyin kare hakkin dan-adam ke mata

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil'adam ta Human rights watch ta fitar akan kasashen 90, ya nuna Najeriya na daga cikin kasashen da aka fi aikata laifukan take hakkin dan'adam a shekarun 2015 da 2016.

Rahoton ya zargi gwamnatin Najeriya da nuna halin ko-in-kula akan matakan da sojojin kasar da sauran jami'an tsaro kamar 'yan sanda suka dauka akan wasu 'yan kasar da suka hada da mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi a birnin Zaria na jihar Kaduna da ma wasu jihohin kasar.

Rahoton ya ce ya kamata matasan da ke tasowa a ba su kwarin gwiwar tunkarar kalubalen da ke gabansu na 'yancin fadar albarkacin bakinsu.

Rahoton ya kuma ba da misali da yadda ya ce 'yan sandan Najeriya sun hallaka mambobin kungiyar IOPB, wanda ke fafutukar tabbatar da jamhuriyar Biafra a lokacin da suke zanga-zanga a watan Fabrairun shekarar da ta wuce, kuma kawo yanzu babu wani jami'in tsaro ko guda da aka gurfanar gaban kuliya domin fuskantar hukunci.

Har ila yau, a watan Disambar 2015, sojojin Najeriya sun hallaka mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi ta Shi'a su kusan 347 wadanda suka zarga da yunkurin hallaka Babban Hafsansu Laftanar Janar Tukur Burutai a birnin Zaria a lokacin Muzahharar da suka saba yi a duk shekara.

Kazalika an yi ta hallaka mambobin kungiyar a jihar Kaduna a lokacin da gwamnatin jihar ta haramtawa 'yan kungiyar gudanar da ayyukansu, a wannan lokaci ne 'yan kungiyar da ke jihohi 4 na arewacin Najeriya suka dauki kwanaki ana tashin hankali tsakaninsu da jamiu'an tsaro.

Babban jami'in kungiyar ta Human rights watch a sashen bincike Moses Segun ya ce bai kamata a kashe mutane ba a lokacin da suke zanga-zangar lumana, kuma bai kamata gwamnati ta yi amfani da karfi akansu ba.

Kungiyar ta cigaba da cewa, idan har gwamnati za ta zuba ido jami'an tsaro na cin karensu babu babbaka, kuma ba a hukunta wadanda aka samu da laifi ba,to ko shakka ba bu rashin zaman lafiya zai karu a tsakanin al'umma.

Kawo yanzu dai hukumomin Najeriya ba su ce komai ba akan rahoton, ko da yake a baya dai sun sha musanta irin wadannan zarge-zarge irin wanda kungiyoyin kare hakkin bil-adama suke yi.