Masu shiga tsakani na Ecowas za su sake komawa Gambia

Yahaya Jammeh da Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ecowas dai ta jingine barazanar sauke Jammeh da karfin soji

Tawagar masu shiga tsakani da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma Ecowas ta dorawa alhakin warware rikicin siyasar kasar Gambia, na shirin komawa kasar ranar Jumu'a.

Tawagar wadda ke karkashin jagorancin Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari za ta yi yunkurin karshen ne na shawo kan shugaban kasar Yahya Jammeh ya sauka daga mulki cikin lumana.

Da farko dai masu shiga tsakanin sun shirya komawa kasar ne a ranar Laraba amma suka dage zuwa Juma'a bayan da shugaba Jammeh ya nemi da su yi hakan.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da Majalisar wakilan Najeriya ta amince kasar ta ba shi mafakar siyasa idan ya amince ya sauka daga mulki ba tare da matsala ba.