Ba abin da zai hana ni zama shugaban Gambia - Barrow

Adama Barrow

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Yanzu haka dai akwai wata kara da Jammeh ya shigar gaban kotun kolin kasar yana kalubantar zaben Barrow.

Wanda ya lashe zaben shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya ce ko ana ha-maza ha-mata sai ya sha rantsuwar kama aiki a zaman shugaban kasar Gambia a makon gobe.

A cikin wata hira da BBC Mr. Barrow ya yi kira ga shugaba mai ci yanzu Yahaya Jammeh da ya zo su tattauna ido-da-ido domin warware rikicin siyasar kasarsu gabanin wannan ranar 19 ga wata Janairu.

Kalaman nasa na zuwa ne sa'o'i gabanin isar tawagar masu shiga tsakanin ta kungiyar Ecowas zuwa kasar domin ciwo kan Yahaya Jameh ya sauka a cikin Lumana.

''Wa'adin mulkinsa zai kare da karfe 12 na dare na ranar 18 ga wata, don haka a hukumance zan kasance shugaban kasar ranar 19 ga wata; kuma ko ana ha-maza ha-mata sai an rantsar da ni'' inji Barrow.