China ta gargadi Amurka game da fito-na-fito kan tsibirai.

Jiragen ruwan kasar China na ta aikin yasar tekun da ke kan tsibiran Spratly.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kasar Chinar na ta gina tsibirai a cikin tekun da wasu kasashen ke ikirarin mallaka.

China ta yi gargadin cewa hana ta amfana da tsibiran da ta gina a cikin tekun da ake takaddama a kai zai haifar da mummunan tashin hankali.

Martnin cikin fushi na zuwa ne bayan kalaman wanda ke sa ran zama sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson dake cewa ya kamata Amurka ta haramtawa China damar amfana da tsibiran dake cikin tekun kudancin China.

Kasar Chinar na ta gina tsibirai a cikin tekun da wasu kasashen ke ikirarin mallaka.

Yayin da yake magana lokacin zaman sauraron tabbatar da shi a matsayin sakataren harkokin wajen a ranar Laraba, Mr Tillerson ya danganta gina tsibiran da Chinar ta yi da hadewar da yankin Crimea na kasar Ukraine da kasar Russia ta yi.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen China Lu Kang, ya maida martanin cewa, China na da 'yancin gudanar da harkokinta na yau da kullum a yankinta.

Bayanan hoto,

Jaridun kasar China biyu sun yi dogon sharhi kan kalaman na Mr Rex Tillerson

Wasu jaridun kasar biyu China Daily da Global Times sun yi sharhi inda suke kakkausar suka game da kalaman Mr Tillerson.

Jaridar ''China Daily'' ta yi hasashen cewa kalaman na shi sun nuna yadda ya jahilci dangantakar da ke tsakanin China da Amurka, da ita kan ta hulddar diplomasiyya.

" Bai kamata a dauki irin wadannan kalamai da muhimmanci ba, saboda ba su da wata madogara,'' in ji jaridar.

Ita kuwa jaridar ''Global Times'' cewa ta yi Mr Tillerson ya furta wadannan kalaman ne don ya samu shiga wurin sanatoci su amince da tabbatar shi a mukaminsa.

Gwamnatin tsohon shugaban Amurka Barack Obama ta nuna adawa da gina tsibiran, amma ba ta taba yin barazanar toshe wa China kafofi ba.

Mr Tillerson dai bai bayyana yadda Amurkar za ta hana kasar China amfana da tsibiran ba, amma duka jaridun kasar biyu sun ce wannan wasu manufofi ne na a-jira-a-gani.