Australia: Minista ta yi murabus kan badakalar kudaden gwamnati

Sussan Ley ta yi murabus daga matsayinta na ministar Lafiya a Australia

Asalin hoton, ABC

Bayanan hoto,

Sussan Ley ta yi murabus daga matsayin ministar lafiya ta kasar Australia

Ministar lafiya ta kasar Australia Sussan Ley ta yi murabus, kan amfani da wasu kudaden gwamnati wajen sayen gida a yankin ''Queensland's Gold Coast.''

Firai Minista Malcolm Turnbull ya ce ya amince da murabus din na Ms Ley ranar Jumma'a .

Badakalar kudade ta dabaibaye harkokin siyasar Australia a cikin shekarun baya-bayan nan.

Yanzu haka Mr Turnbull ya yi alwashin kafa hukumar sa ido mai zaman kan a bisa tsarin Birtaniya, wajen lura da kudaden da ake kashewa a majalisar dokoki.

Ya kuma ce "'Yan kasar Australia na da 'yancin su ga cewa an yi taka-tsan-tsan wajen kashe kudaden gwamnati, tare da tabbatar da cewa an yi amfani da su wajen ayyukan jama'a yadda ya kamata,''

"Ya kamata mu yi duk yadda za mu yi wajen yin taka-tsan-tsan da kudaden gwamnati.''

A jawabinta na murabus, Ms Ley ta jajirce a kan cewa bata karya wata doka ba.

Kana ta ce wannan rudani ya zama wani abu da ke dauke hankalin gwamnati.