Johanna Konta ta doke Agnieszka Radwanska a gasar Sydney International

Johanna Konta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Konta za ta fafata da Kirsten Flipkens a zagayen farko na gasar Australian Open

Gwarzuwar 'yar kwallon Tennis ta Birtaniya Johanna Konta ta lashe gasar Sydney International ranar Juma'a inda ta yi nasara a kan Agnieszka Radwanska da ci 6-4 6-2 a kasar Australia.

Konta, wacce ita ce ta goma a duniya a fagen Tennis, ta doke takwararta 'yar kasar Poland a zagaye na uku.

'Yar wasan mai shekara 25 ta mamaye wasan a gaban Radwanska, wacce take matsayi na uku a duniya, inda ta yi wasa cikin gwanancewa da kuma doka kwallo a kai-a kai.

Bajintar da ta nuna za ta bai wa Konta kwarin gwiwar daukar kofin Grand Slam na farko inda za ta kara da Kirsten Flipkens a gasar cin kofin Australian Open a makon gobe.

Ta kai matakin kusa da na karshe a Melbourne Park a shekarar 2016, koda yake ta sha kashi a hannun Angelique Kerber, wacce ta dauki kofin.

A baya dai Radwanska ta doke Konta, ciki har da a wasan karshe na gasar China Open.