Muna fatan sayen Saido Berahino — Mark Hughes

Saido Berahino

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Saido Berahino ya zura kwallonsa ta karshe ne a wasan da suka yi da Chelsea ranar 27 ga watan Fabrairu

Kocin Stoke City Mark Hughes ya ce yana fatan kungiyar za ta sayi dan wasan gaba na West Brom Saido Berahino idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallo a watan Janairu.

A lokacin bazara ne kungiyar ta taya dan wasan mai shekara 23, a yayin da Stoke suka yi tayin sabunta kwantaraginsa a karo na uku a watan jiya.

Berahino bai buga wa kungiyar wasa ba tun daga ranar 10 ga watan Satumba, kuma an aike da shi zuwa Faransa domin ya samu horo kan yadda zai rage kiba.

Hughes ya ce, "Muna son sayen sa, kamar yadda wasu kungiyoyin ke son yi. Ina fata za mu saye shi."

Kwantaragin Berahino zai kare a Stoke City a karshen kakar wasa ta bana, kuma tun bazarar da ta wuce ne kungiyar Albion na tattaunawa da shi domin yiwuwar sayen sa.