'Yar Hungary da ta wulakanta 'yan gudun hijira na kurkuku

Petra a lokacin da take tade wasu 'yan gudun hijira

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Petra Laszlo ta ce zata daukaka kara

An daure wata mai daukar hoto 'yar kasar Hungary tsawon shekara uku a gidan yari a kasar bayan an kama ta aa laifin rashin da'a.

Mai daukar hoton ta rika duka da kafa tare da taɗe wasu 'yan gudun hijira dake kusa da iyakar Hungary da Serbia.

A watan Satumban shekarar 2015 ne Petra Laszlo ta aikata laifin a lokacin da 'yan gudun hijirar ke kokarin kutsawa ta cikin 'yan sandan da suka tsare hanyar da suke so su wuce.

An dauki hotonta tana dukan mutane biyu da kafa a lokacin da suke tserewa, ciki har da karamar yarinya. Daga bisani kuma ta taɗe wani mutum mai dauke da wata yarinya.

Alkali Illes Nanasi yace abin da ta aikata ya saba wa tarbiyar al'ummarsu, kuma yayi watsi da lafuzan lauyoyin dake kare ta da suka yi na cewar tana kokarin kare kanta ne .

Ta ce " na juya sai naga daruwawan mutane sun yiwo kaina. Na tsorata matuka".

Petra dai ta bayyana ne a kotun gundunmar Szeged, inda aka saurari karar a bidiyo kuma daga lokaci zuwa lokacin ta kan fashe da kuka.

Ta ce tana samun barazanar kashe ta bayan anyi kamfen nuna kyama a kan abinda ta aikata".

Gidan talabijin na masu sassaucin ra'ayi ta kore ta daga aiki bayan bidiyon abinda ta aikata ya bazu a shafukan sada zumunta.

Ta ce zata daukaka kara.