South Korea ta hana zubda cikin 'ya mace

Yara mata a Koriya ta kudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A baya a al'adance an fi daraja yara mata fite da maza a kasar Korea ta kudu

A yaran da ake haifa a India, akwai adadin 'yaya mata 100, inda maza kuma ke kai wa 111, a kasar china kuma yaran da ake haifa akwai dadin mata 100, kana na maza ke kai wa 115.

Wata kasa daya ce ta samu kusan irin kwatankwacin alkaluman kasashen Indiyan da China a shekarar 1990, amma kuma tun a wancan lokacin, ta kawo daidaito a jinsin mutanenta.

Ta ya Koriya ta kudu ta yi hakan?

"Yarinya mace daya daidai take da maza 10" wannan shine sakon da gwamnatin Koriya ta kudu ke bazawa.

A shekaru 20 da suka gabata a lokacin da daidaito a jinsin dan adam ke da yawa, haihuwar yara maza ya kai 116 yayinda na mata ya kai 100.

An shafe karni da dama ana fifita soyayyar yara maza a kan mata a al'adar Koriya ta kudu.

Ana ganinsu a matsayin masu daukar nauyin dangi da taimakawa da kudi da kuma bai wa iyayensu kulawa a lokacin da suka tsufa.

"Suna kallon mace a matsayin wacce bata cikin danginta, daga lokacin da ta je gidan mijinta, a cewar Ms Park-cha Okkyung, darakatan tarayyar kungiyar mata ta Koriya ta kudun.

Gwamnati ta kasance cikin neman mafita cikin gaggawa.

A wani yunkuri na rage zubda ciki idan har mace ta gano cewa ba jinsin da take so ta haifa bane, Koriya ta Kudun ta samar da wata doka wadda ta haramtawa likitoci su bayyana jinsin ɗa ga mata masu juna biyu.

A dai-dai wannan lokaci kuma mata na kara samun cigaba a ilimi inda da dama daga cinkinsu suka fara aiki kuma suna kalubalantar al'adar cewar namiji ne zai ciyar tare da biya wa iyalinshi bukatunsu.

Wannan hanyar da aka bi ta yi aiki, amma ba saboda da dalili daya ba kawai, sai dai dalilan wasu abubuwan sun kai ga daidaito a tsakanin jinsi.

A wani rahoto da bankin duniya ya fitar, an yi amannar cewa kasar Koriya ta kudu ce kasa ta farko a Asiya da ta sauya rashin daidaito a haihuwar yara maza da mata.

Karin mutanae a birane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Har yanzu ana so mata su hada aikin ofis da kula da iyali a lokaci guda a kasar Koriya ta Kudu.

Haramtawa a hukumance zai iya rage abubuwa kadan, amma kuma Monica Das Gupta, da ke koyarwa a jami'ar Maryland dake Amurka ta ce shekera 7 bayan dokar, mata sun cigaba da zubda cikin jinsin da basa so.

Ta dangata sauyin ne da yadda mutane ke ƙaruwa a birane a Koriya ta kudun.

A cikin sama da shekara goma mutane da dama sun koma suna zama a cikin rukunin gidaje a birane tare da mutanen da basu sani ba kuma har ila yau suna aiki a masana'antu tare da mutanen da basu sani ba.

Sai dai har yanzu, China da Indiya na da rashin daidaito sosai a jinsin mutane, duk da rashin doka a Indiya da kuma irin yadda China ke yin hani ga batun gwajin zaben jinsi da kuma zub da ciki.

An samu cigaba

An samu cigaba sosai a kan yadda mata ke tunani, saboda a yanzu mazan koriya sun ilimantu, kuma kansu ya waye.

Mutanen da suka manyata ne kawai ke nuna fifiko ga 'yaya maza.