Faransa da Jamus sun tsinci kansu a cikin dusar kankara

Faransa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Lion-sur-Mer, arewacin Faransa: Normandy gabar teku na fama da dusar kankara

Guguwar dusar kankara ta mamaye yankunan gabashin Turai, tare da haddasa katserwar wutar lantarki a gidaje da dama, da karya itatuwa, da haifar da cikas ga harkokin sufurin jiragen kasa.

A kasar Faransa katsewar wutar lantarkin ta shafi gidaje fiye da 237,000, yayinda guguwar ta mamaye fadin Normandy da yankunan dake arewacin Faransar.

Daga bisani guguwar kankarar yiwa lakabi da "Egon", ta abkawa kudancin kasar Jamus - musamman Rhineland-Palatinate, da arewacin Bavaria.

Katsewar wutar lantarki da cunkoson ababan hawa sun mamaye sassa da dama.

Jami'an shirin ko-ta-kwana na ta aiki ba dare ba rana a kasashen Faransa da Jamus

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana mukumukun sanyi a birnin Romania.

Duk da hakan, an yi kokarin kare Belgium a gabar teku daga ambaliyar ruwa.

Sanyi ya bazu a fadin Turai da ya zama sanadiyar mutuwar mutune fiye da 65.

Poland da kasashen kudu maso gabashin Turai, har da Romania, da Bulgaria, da Girka da yammacin Turkiya, na fama da dusar kankara da kuma yanayin mukumukun sanyi.

Dubban masu gudun hijira a yankin Balkans da ba su da kariya daga wannan dusar kankara har yanzu suna cikin tanti.