Amurka: Trump ya yi alwashin bayyana rahoton kutsen kasar Russia

Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Donald Trump ya dau alkawarin bayyana sakamakon binciken zargin kutse a harkar zabe

Donald Trump ya yi alkawrin bayyana sakamakon bincike cikin kwanaki 90, kan zargin da ake yiwa kasar Russia na yin kutse lokacin yakin neman zaben shugaban kasa a Amurka.

Shugaban Amurka mai jiran gadon ya bayyana a shafin shi na Twitter cewa: ''Wannan shaci-fadin masu son cimma burin siyasa ne''

Hukumomin leken asirin Amurka sun zargi Rasha da yin katslandan a harkar zaben ta hanyar yin kutsen bayyanan jam'iyyar.

Suna cewa fadar gwamnatin Rasha nada wasu bayanai da ba za a so gani ba game da shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump.

A ranar Alhamis ne shugaban mai jiran gado ya ce daraktan hukumar leken asiri James clapper, ya kira shi don yin " watsi da rahotanin karyar" wanda aka watsa zuwa kafofin yada labarai a baya a cikin makon nan.

Mr Clapper ya ce, ya shaidawa Mr Trump cewa har yanzu ba a yanke hukunci kan sahihancin rahotonnin ba.

Ya kuma musanta zargin da ake yi wa hukumar leken asirin cewa ita ta kwarmata bayanan ga jama'a.