Hare-haren bam sun kashe mutane 11 a jihar Adamawa

Sojoji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojojin hadin-gwiwa sun sha alwashin murkushe Boko Haram

Gwamnatin jihar Adamawa ta ce mutane 11 ne aka tabbatar sun mutu a cikin tashin wasu bama-bamai uku da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram da dasawa a garin Madagali na jihar da ke arewa maso gabashin Nigeria.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Ahmed Sajo, wanda ya tabbatar wa da BBC kai harin, ya ce lamarin ya faru ne ranar Juma'a da safe a wajen da maharba ke tsayawa domin yin bincike da wata matattarar motoci da kuma kusa da inda sojoji suke a garin.

Kwamishinan ya ce 'yan ƙunar-bakin-wake huɗu ne suka kai hare-haren ɗauke goyon jarirai 2, kuma al'amarin ya yi sandin mutuwarsu da wasu fararen hula 5.

Ko da yake kawo yanzu kungiyar ba ta fito ta dauki alhakin harin ba, sai dai a baya garin na Madagali ya sha fama da hare-haren 'yan Boko Haram din.