Hull City ta karbi aron Oumar Niasse da Evandro

Oumar Niasse

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Oumar Niasse

Kungiyar kwallon kafar Hull City ta karbi aron dan wasan gaba na Everton Oumar Niasse zuwa karshen kakar wasa ta bana da kuma dan wasan tsakiya na Porto Evandro a kan kudin da ba ta bayyana ba.

Kungiyar ita ce ta karshe a teburin gasar Premier kuma wannan shi ne karon farko da take sayen 'yan wasa tun bayan sayen koci Marco Silva wanda ya maye gurbin Mike Phelan a watan Janairu.

Dan wasan kasar Senegal Niasse, mai shekara 26, ya koma Everton a watan Fabrairu a kan £13.5m sai dai ya kasa ci musu wasa.

Shi kuwa dan kasar Brazil Evandro, mai shekara 30, ya buga wa Porto wasannin gasar zakarun Turai.

Silva ne kocin Evandro lokacin da yake kulob din Estoril na Portugal.

Hull ba ta yi nasara a wasan Premier tun ranar shida ga watan Nuwamba, kuma ranar Asabar za su fafata da Bournemouth a gida.