Shugaba Buhari yana sa ran shawo kan dambarwar siyarsa kasar

Buhari a Gambia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya kai ziyara Gambia a watan jiya domin shawo kan Mista Jammeh ya sauka daga karagar mulki.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sauka a Gambiya domin sasanta wutar rikicin da ke rurawa a kasar tsakanin shugaba mai barin gado, Yahya Jammeh, da shugaba mai jiran gado, Adama Barrow.

Kakakin shugaban Nigeria, Femi Adeshina ne ya tabbatar da hakan bayan shugaban ya sauka a Banjul, babban birnin Gambia.

Yahya Jammeh, wanda ya shugabanci kasar Afirka ta yamman na tsawon shekara 22, ya amince da shan kaye a zaben da aka yi a watan jiya amma daga bisani ya yi watsi da sakamakon zaben.

A watan jiya ma shugaban Najeriya ya ziyarci kasar tare da wasu takororinsa na Afirka ta yamma domin samun mafita a rikicin siyasar kasar. Amma tafiyar ta su bata yi nasara ba.