Me za ku iya tunawa da shi game da rayuwar 'ya'yan Obama a White House?

Mun duba wasu hotunan rayuwar Malia da Sasha Obama a fadar shugaban kasar Amurka, White House tsawon shekara takwas da mahaifinsu ya yi yana kan mulki.

Bayanan hoto,

Malia Obama na da shekara 10, yayin da kanwarta Sasha ke da shekara bakwai lokacin da aka zabi mahaifinsu a matsayin shugaban kasar Amurka.

Bayanan hoto,

Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden yana tattaunawa da Sasha a ranar da ake rantsar da shi

Bayanan hoto,

Sun bar gidansu da ke Chicago inda suka koma Washington - wannan hoton na nuna Sasha tana leken waje daga tagar mota bayan sun sauke 'yar uwarta a ranar farko da aka kai ta sabuwar makarantar da ta shiga.

Bayanan hoto,

An ba su wani kare mai suna Bo, wanda sau da dama ya rika fitowa baiar jama'a.

Bayanan hoto,

Ranar bikin Easter a White House. A wannan bikin na shekarar 2010, Shugaba Obamaya nunawa Sasha yadda za ta dora hannunta a kan kirjinta idan ana rera taken kasa.

Bayanan hoto,

Wani abu da iyalin Obama suka mayar tamkar dabi'a shi ne yin bikin ranar nuna godiya ga Allah, wato Thanksgiving , inda ake nuna 'yafiya ga talo-talo' - wato ba za a yanka su domin cin namansu ba.

Bayanan hoto,

Malia da Sasha sun raka mahaifansu a tafiye-tafiyen da suke yi zuwa kasashen duniya, cikin su har da rakiyar da suka yi musu zuwa kasashen Ghana, Argentina, France, China da Birtaniya - da kuma Afirka ta Kudu, inda suka karanta kagaggun labarai ga wasu yara a birnin Johannesburg.

Bayanan hoto,

Obama ya yi fice wajen rera waka - a wannan hoton shi ne yake rera wa mai dakinsa waka domin bikin tunawa da zagayowar ranar haihuwarta lokacin da ya kai ziyara wata makaranta a Washington DC.

Bayanan hoto,

Duk da yake a yawancin lokuta Malia da Sasha na cikin murmushi, amma a wasu lokutan a kan gan su ba tare da kuzari ba ko kuma suna nuna gajiyawa - kamar a wannan hoton bikin nuna goyon baya ga dakarun sojin Amurka.

Bayanan hoto,

Barack Obama ya sake tsayawa takara a zaben da ya lashe a shekarar 2012.

Bayanan hoto,

Malia da Sasha yayin da suke daukar hoton dauki-kanka ranar da aka sake rantsar da mahaifinsu a matsayin shugaban kasa.

Bayanan hoto,

Ranar bikin Kirsimeti a fadar White House inda Obama da 'ya'yansa da kuma mai dakinsa suka dauki hoto tare da yara.

Bayanan hoto,

A shekarar 2011, an yi taro da shahararrun mawaka,cikin su har da Justin Bieber.

Bayanan hoto,

Obama da 'ya'yansa a ranar nuna godiya ta shekarar 2015, amma ba su fito ba a ranar nuna godiyar ta 2016, inda Obama ya ce sun ki fitowa ne saboda kada ya ba su 'kunya'