Majalisa ta dauki matakin soke shirin inshorar lafiyar Obama

US hospital

Asalin hoton, Getty Images

Majalisar wakilan Amurka ta dauki matakin farko na soke shirin inshorar lafiya da Shugaba Barack Obama ya sanya wa hannu.

'Yan majalisar a karkashin jam'iyyar Republican sun amince da wani kasafin kudi da zai bayar da damar a samar da wani kudirin doka da zai soke shirin - wanda 'yan jam'iyyar Democrat ba za su iya hanawa ba.

Sai dai 'yan majalisa daga dukkan jam'iyyun na nuna fargabar su kan rashin kaddamar da wani shiri da zai maye gurbin shirin inshorar da ake yi wa lakabi da Obamacare.

Hakan dai ya sanya babbar alamar tambaya kan yadda za a kula da marasa lafiya Amurkawa fiye da miliyan ashirin bayan an soke shirin.

'Yan majalisa na bangaren Republican 277 ne suka amince da kasafin kudin, yayin da 'yan Democrat 198 suka yi fatali da shi, abin da ke nuna cewa za a yi watsi da babban shirin Shugaba Obama, mako guda kafin ya sauka daga mulki.

'Yan majalisar dattawa 51 ma sun amince a yi watsi da shirin yayin da 48 suka ki amincewa da soke shi a kuri'ar da suka kada ranar Alhamis.

A ranar Juma'a ne shugaban kasar mai jiran gado, Donald Trump, ya wallafa sako a shafinsa na Twitter inda yake cewa: "Nan gaba kadan ne shirin inshorar lafiya mai tsada na Obama zai zama tarihi!"

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kakakin majalisar wakilai Paul Ryan