Gambia: Buhari da Barrow sun fice zuwa Mali

Shugaba Muhammadu Buhari wanda ke jagorancin tawagar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan majalisar dokokin Nigeria dai sun amince a ba Jammeh mafaka a kasar idan ya amince ya sauka.

Tawagar shiga tsakani da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (Ecowas) ta tura zuwa kasar Gambia domin matsa wa shugaba Yahaya Jammeh lamba ya sauka; ta isa birnin Bamako na kasar Mali tare da shugaban kasar mai-jiran-gado Adama Barrow.

Tawagar wadda Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ke jagoranta, za ta yi wa uwar kungiyar bayani ne kan sakamakon ganawarsu da shugaba Jammeh wadda ga alamu ba ta yi armashi ba.

Shugabannin kasashen kungiyar ta Ecowas wadanda ke wani taro yanzu haka a babban birnin kasar ta Mali ne suka bukaci su gana ido-da-ido da shugaban Gambia mai-jiran-gado Adama Barrow.

''Bayan tawagar ta yi ma ta bayanin ne kungiyar ta ECOWAS za ta yanke shawara kan mataki na gaba da za ta dauka'' in ji Ministan Harkokin Wajen Nigeria Geofrey Onyeama lokacin yake yi wa manema labarai kan sakamakon tattaunawar a birnin Banjul.

Tuni dai kungiyar Tarayyar Afrika (AU) ta ce daga ranar 19 ga wannan watan za ta dai na martaba Yahya Jammeh a matsayin shugaban kasar Gambia.