Boko Haram: Sojojin Nigeria 3 sun mutu a fagen daga

Sojojin Nigeria a fagen daga
Bayanan hoto,

Tuni da aka kwashe gawwakin sojojin tare da wadanda suka raunata zuwa asibiti.

Rundunar Sojan kasa ta Najeriya ta ce sojojinta uku sun mutu wasu kuma 27 suka samu raunukka a cikin wata bata-kashi da mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

Sai dai ta ce su ma mayakan kungiyar ta Boko Haram 10 sun mutu wasu kuma da yawa sun samu raunukka a cikin arangamar wadda aka yi a yankin Kangarwa da ke jihar Borno da ranar Alhamis da daddare.

Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce an fara musayar wutar ne tsakanin sojojin kasar da mayakan na Boko Haram tun da marece har cikin dare.

Sanarwar wadda Mukaddashin Daraktan watsa labarai na rundunar Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya saka wa hannu, ta ce fadan ya soma ne bayan da mayakan na Boko Haram suka kai farmaki kan wani sansanin sojojin da ke yankin na Kangarwa daga gabar Tafkin Chadi.

Ta ce sojojin da taimakon jiragen yaki na rundunar sojan sama sun yi nasarar fattakar maharan inda har suka kashe goma daga cikinsu suka kuma suka kwato makamai daga iri daban-daban daga garesu.