Trump ya ce a shirye yake ya yi aiki da Russia da China

Zababben shugaban Amurka Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zababben shugaban Amurka Donald Trump na yin nuni game da manufofinsa kan kasashen waje.

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya ce a shirye yake ya yi aiki da kasashen Rasha da China, muddin suka bayar da hadin kai.

Mr Trump ya shaida wa mujallar Wall Street Journal' cewa sabon takunkumin da aka kakaba wa kasar Rasha zai ci gaba da zama daram, ''akalla na dan wani lokaci'' amma za a iya cire shi.

Ya kuma ce za a yi zaman tattaunawa kan manufofin nan na China-kasa-daya, wanda Amurka ba ta yi amanna da kasar Taiwan ba.

A cewarsa kwamitin majalisar dattawan Amurka zai binciki batun hannun da ake zargin kasar Rasha da shi na yin katsalandan a harkokin zaben shugaban kasar.

Mr Trump ya ce za a iya dage takunkumin kasar ta Russia, muddin ta taimakwa Amurka a yakin da take yi da tsattsauran ra'ayin addinin Islama da sauran batutuwa.

Ya kara da cewa, "Muddin Rasha na taimaka mana, me zai sa a kakabawa wani takunkumi idan yana aikata abubuwan alkhairi?