Amurka: Mun yi farin cikin gano diyarmu bayan shekaru 18 da sace ta

Kamiyah Mobley lokacin tana jaririya da matar da aka kama Gloria Williams

Asalin hoton, Ofishin Jacksonville Sheriff

Bayanan hoto,

Kamiyah Mobley lokacin tana jaririya da matar da ta sace ta, Gloria Williams

Kakar yarinyar da aka sace sama da shekaru 18 da suka gabata lokacin tana jaririya na kukan murnar gano ta da aka yi.

Velma Aiken ta shaidawa BBC cewa tana matukar farin cikin cewa Kamiyah Mobley na cikin koshin lafiya.

An gano Kamiyah a Florida, tare da cafke wata mata mai shekaru 51 da ta sace ta , kamar yadda 'yansanda suka bayyana.

Mahukunta a Walterboro dake jihar South Carolina, na tuhumar Gloria Williams, kan sace yarinyar cikin watan Yunin shekara ta 1998 a wani asibiti dake Jacksonville a jihar Florida ta Amurka.

Ms Mobley ta kasance tare da Ms Williams da ta dauka a matsayin ita ce mahaifiyarta.

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto,

Kamiyah Mobley (Hagu), tare da matar da ta dauka ita ce mahaifiyarta

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Ms Aiken (Dama) kakar Kamiyah ta ce za ta samu lokaci ta zauna da jikarta

Kakar Kamiyah Velma ta ce iyalai duka sun samu yin magana da jikarta, inda suka gabatar mata da kan su, kuma Ms Mobley ta yi alwashin haduwa da su.

" Babu abinda nake yi sai kukan farin ciki, sanin cewa an same ta cikin koshin lafiya,'' In ji Ms Aiken said.

Kakar ta kara da cewa ta dade tana tunanin cewa jikarta na nan da ranta, kuma duk wanda take tare da shi na kula da ita.

" Mun kawai ci gaba da addu'oi tare da yin fatan sake ganinta,'' ta ce.

Ofishin hukumar tsaro na Jacksonville Sherriff ya ce gwajin kwayoyin halittun da aka yi ya tabbatar da asalin Ms Mobley.

Ya kuma ce tun bayan da aka sace jaririyar sun bi diddigin bayanan sirri 2,500 da suka rika samu.

Matar da ta sace Kamiyah ta shaidawa mahaifiyarta Shanara cewa, jaririyarta na fama da zazzabi kuma tana bukatar a duba ta.

Ta dauke ta zuwa waje inda daga nan ta gudu da ita.

Batun ya ja hankulan kafafan yada labarai, yayinda Shanara ke kokarin gano diyarta.

Duk da cewa an sanar da iyayenta na asali cewa an gano ta, kuma sun yi ''farin ciki'', ofishin Jacksonville Sherriff ya ce '' ya rage na wannan yarinya yadda ta ke so a yi, tun da yanzu ta mallaki hankalinta''

Jacksonville Sheriff Mike Williams ya ce: " Tana da masaniya cewa me yiwuwa wani abu ya faru.''

" An sace ta tun tana jaririya, don haka tana bukatar a bata lokaci...Muna son mutunta duk wasu sirrinta, don haka kuma muna son ku yi hakan.''

Sa'oi takwas da haihuwar jaririyar ne, lokacin da wata mata da ta yi bad-da-kama a matsayin ma'aikaciyar lafiya a wani asibiti mai suna UF Health Jacksonville ta sace ta.