Mayar da ofishin jakadancin Amurka Jerusalem zai haifar da rikici — Mahmoud Abbas

Paparoma Francis (Dama) yana shan hannu da shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas a fadar Vatican, birnin Vatican City, 14 ga watan Janairu 2017.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mahmoud Abbas (Hagu) ya yi wadannan kalaman ne bayan ganawarsa da Paparoma Francis a karo na uku.

Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas ya gargadi Amurka cewa za a shiga rudani muddin shugaba mai jiran gado Donald Trump ya aiwatar da shirinsa na mayar da ofishin huddar jakadancin kasar a Isra'ila zuwa birnin Kudus.

Ya fadi hakan ne lokacin kaddamar da ofishin huddar jakadancin Palasdinu ga Holy See, bayan ganawar sa da Paparoma Francis.

A shekara daya da rabi da ta gabata ne fadar Vatican ta amince da kasancewar Palasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Palasdinawa na kallon gabashin Kudus wanda zai kasance babban birnin kasar su a nan gaba, amma kuma Isra'ila na ayyana daukacin birnin a matsayin na ta

A shekara ta 2015 ne dangantaka tsakanin Holy See da yankunan Palasdinu ta kara karfi, tare da rattaba hannun yarjejeniyar amincewa da Palasdinu a matsayin kasa- matakin da ya harzuka Isra'ila.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Paparoma Francis ya dadadawa shugaban Palasdinawa rai wajen ambaton Palasdinu a matsayin kasa, lokacin wata ziyarar kwanaki 3 a shekara ta 2014

Dangataka tsakanin Isra'ila da fadar Vatican ta kara tsami, bayan da Paparoma Francis ya bayyana shugaban Palasdinawa a matsayin '' mai son zaman lafiya'' a lokacin wani biki a fadar ta Vatican.

A ranar Lahadi ne Faransa za ta karbi bakuncin taron kasa da kasa a birnin Paris, don fara tattaunawa kan zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Paparoman ya sha nanata goyon bayansa kan matakin fara tattaunawar zaman lafiyar.