Ana fargabar mutuwar 'yan ci-rani 100 a tekun Bahar Rum

Misalin yadda 'yan ci-rani ke makare jirgin ruwa a tekun

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Ana aikin neman mutanen ne a cikin wani yanayi mai wahala

Kimanin fasinjoji 100 ne suka bace a tekun Bahar Rum bayan da jirgin suke tafiya a ciki ya nutse daura da gabar ruwan kasar Libya.

Dogarai masu tsaron gabar tekun Italiya, wadanda ke aikin laluben mutanen, sun ce sun tsamo gawawwakin mutane takwas da kuma wasu hudu a raye.

Amma sun yi imanin akwai wasu gommai da ba a gano ba har duhun dare ya kankama.

Jirgin dai ya nutse ne a ruwan da ke tsakanin kasashen na Libya da Italiya kuma kawo yanzu ba a san kasashen da mutanen suka fito ba.

Hukumar Kula da 'Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce a bara kadai mutane 5,000 ne suka mutu a wannan tekun garin kokarin tsallakawa zuwa nahiyar Turai.